Dalilan da yasa kotu ta umarci da a yiwa Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara gwajin kwakwalwa

0 275

Wata kotun musulunci da ke shari’ar Malamin addinin nan Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da na kunne a wani zaman cigaban shari’ar da ake yi masa a jihar Kano.

Kotun ta bayar da umarnin ne bayan Malamin addinin Musuluncin ya gaza amsa tambayoyin da alkalin kotun Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa a zaman kotun na yau.

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin batanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Tun da safe aka soma zaman kotun da ke Kofar Kudu kusa da gidan Sarkin Kano tare da gabatar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan wanda ake zargi.

Lauyoyin da ke kare Mallam Abduljabbar karkashin jagorancin Barista Sale Bakaro sun soki yadda ake tsawaita shari’ar da kuma sabbin tuhume-tuhumen da aka gabatar kan Malamin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: