Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa bata biya kungiyar ASUU kudaden gyaran jami’u ba da kuma sauran bukatun su.
Ministan ilimi Emeka Nwajiuba shine ya bayyana haka lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, inda yace gwamnatin tarayya na duba yadda zata biya kungiyar ASUU kudaden da take bukata daga babban bankin kasa CBN.
Sai dai ana ta bangaren kungiyar ta ASUU batayi maraba da kalaman na ministan ilimin ba, inda ta bayyana cewa akwai rashin gaskiya da kuma rashin mutunta muradan kungiyar ta su.
A shekarar 2020 kungiyar ta shiga yajin aiki na watanni tara, wanda suka fara a watan mayu zuwa watan disamba, wanda hakan ya kawo nakasu matuka a harkokin ilimi.
A ranar biyu ga watan agustan wannan shekarar, ministan kwadago Dr chris Ngige yace gwamnatin tarayya ta biya malaman jami’o’un hakkokin su cikin wata takarda mai dauke da sa hannun malaman.