Attajirin da ya mallaki kamfanin Macrosoft Bill Gates da uwargidan sa Melinda sun bayyana shirin raba auran su bayan kwashe shekaru 27 suna tare.
Bill da Melinda Gates da suka mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 130 suka kuma kaddamar da wani sashe daga cikin ta wajen aikin jinkai sun sanar da shirin raba auran su ne a yammacin jiya bayan kwashe shekaru 27 suna tare.
Yayin sanar da matakin ma’aurantan sun ce rabuwar su ba za ta hana su ci gaba da aiki tare ta hanyar Gidauniyar su ta Bill and Melinda Gates ba, gidauniyar da ke taimakawa ta hanyar kula da lafiya da daidaito tsakanin mata da maza da ilimi da kuma wasu hanyoyi na daban.
Sanarwar hadin gwuiwar da suka gabatar ta ce bayan dogon nazari da kuma aiki sosai akan dangantakar da ke tsakanin su, sun yanke hukuncin kawo karshen auran su.
Sanarwar ta ce a cikin wadannan shekaru 27 sun reni yara guda 3 da gina Gidauniyar da ke aiki a kowanne sashe na duniya domin tabbatar da mutane na rayuwa cikin koshin lafiya da bayar da gudumawa.
Sanarwar ta bukaci jama’a da su mutunta matakin da suka dauka da kuma basu sarari domin fara wata sabuwar rayuwa.
Bill mai shekaru 65 ya gamu da Melinda a shekarar 1987 a kamfanin Microsoft, kuma suka yi aure a shekarar 1994.