Dalilan da yasa ASUU ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

0 210

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta zargi Gwamnatin Tarayya da ofishin Babban Akanta na Najeriya da muzgunawa mabobinta ta hanyar jan kafa wajen biyansu hakkokinsu duk kuwa da yarjejeniyar da aka cimma a kan haka.

Kungiyar ta yi zargin cewa basussukan da mambobin nata ke bi sun kama daga watanni biyu zuwa 10.

Shugaban kungiyar reshen Jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole wanda ya tabbatar da hakan a Ibadan ya kuma zargi gwamnatin da taurin bashi da kuma jan kafa wajen mutunta yarjejeniyar da suka cimma da ita.

ASUU ta yi gargadin cewa la’akari da matsin tattalin arziki, idan tura ta kai bango, to babu makawa za su sake tsunduma yakin aikin.

Farfesa Akinwole ya ce hatta a Jami’ar ta Ibadan, akwai sama da malamai 100 da ke bin bashin albashin kusan watanni 10.

Ya ce sabbin ma’aikatan da aka dauka a watan Fabrairu har yanzu ko sisi ba su samu ba saboda suna nan a kan bakarsu kan batun tsarin biyan albashi na IPPIS.

Shugaban kungiyar ya kuma zargi gwamnatin da ci gaba da zabtare kudaden ma’aikata da sunan samar da gidaje duk da ba su nuna sha’awar yin hakan ba.

https://aminiya.dailytrust.com/taurin-bashi-asuu-ta-yi-barazanar-sake-tsunduma-yajin-aiki

Leave a Reply

%d bloggers like this: