Dalibi dan asalin jihar Jigawa ya zama zakara a gasar dalibai ta duniya kan sabuwar fasahar (AI)

0 323

Zulkiflu Abdullahi Dagu

Dalibin Aji na 5 a sashen Nazarin harhada Kwamfuta a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Abdullahi Ahmad Bello, wanda dan asalin jihar Jigawa ne, ya zama zakara a gasar dalibai ta duniya kan sabuwar fasahar (AI) da aka gudanar a kasar China.

Abdullahi wanda ya fito daga karamar hukumar Babura, ya fara da tsallake shamakin zama gwarzo a matakin rukuni, wadda ta gudana a kasar Afirka ta Kudu.

Kwamashinan a ma’aikatar ilimi mai zurfi ta Jihar Jigawa Dr. Isah Yusuf Chamo, shine ya gabatar da Dalibin ga gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi, wanda yace Abdullahi yayi nasarar doke abokan karawarsa daga kasashe 42 na Duniya.

Da yake jawabi gwamna Namadi ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta baiwa daliban, tallafin karo karatu a matakin Digiri na 2 da na Uku da zarar sun kamala karatu, inda yace gwamnati da al’ummar Jigawa za su ribaci basirar da matasa ke da ita a fannin fasahar zamani. A karshe matasan biyu, sun shelanta sabbin dabarun da suke kirkira da zasu taimaka wajen ganowa da magance matsalolin Kansar mama, da matsalar Ambaliya, wadda ake sa ran fasahar za tayi amfani da manyan yarukan Hausa da Yoruba da kuma Turancin Ingilishi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: