Dakatar da aikin hayar mota a filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja zai sa matafiya shiga tsaka mai wuya
Matafiya na iya shiga tsaka mai wuya yayin da hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN ta dakatar da aikin hayar mota a filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar Abdullahi Yakubu-Funtua ya sanyawa hannu a jiya.
Funtua ya ce hakan ya biyo bayan rikicin bangaranci da ba a warware ba a tsakanin masu aikin hayar motocin da ke shafar ayyukan hayar motocin a filin jirgin.
Hukumar kula da filayen saukar jiragen sama ta ce dakatarwar ya zama dole kuma ta bukaci matafiya da su yi amfani da wasu hanyoyin sufuri ko isar da sako ta wayar tarho a ciki da wajen filin jirgin. Hukumar ta FAAN ta yi nadamar rashin jin daɗin dakatarwar da ka iya haifar da kalubale ga manyan fasinjoji, masu amfani da filin jirgin da sauran jama’a.