Dakarun Operation Hadin Kai Sun Fatattaki Mayakan Boko Haram A Dajin Sambisa

Dakarun Operation Hadin Kai sun fatattaki mayakan kunghiyar Boko haram a maboyar su dake Dajin Sambisa a karamar hakumar Bama dake jihar Borno, inda suka kashe akalla mayaka 18.
An rawaito cewa dakarun sun samu bayanai daga sashin fikira na sabon sansanin mayakan, inda suke shirya ayyukan da suke kaddamarwa a yankunan Sheutari da Mutari.
An tattaro cewa dakarun runduna ta 21 hadin guiwa da jamia’n sa kai a ranr takata data gabata sun kaddamarda wani hari kan sansanin mayakan dake garin Ba’aba inda suka tarwatsa sansanin.
Idan dai za’a iya tinawa an hallaka daruruwan mayaka a baya-bayan nan a yankunan Sheutari da Mutari sakamakon wani fada tsakanin wasu kungiyoyi da basa ga maciji da juna.