Dakarun Operation Delta Safe sun rusa haramtattun matatun mai guda 22 a cikin makon da ya gabata

0 79

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Delta Safe sun cafke mutane 49 da ake zargi da laifin satar mai da kuma rusa haramtattun matatun mai guda 22 a cikin makon da ya gabata.

Babban Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojoji, Manjo-Janar Markus Kangye ne ya bayyana hakan cikin rahoton mako-mako a Abuja, inda ya ce an dakile satar mai da kudinsa ya kai naira miliyan 869.2.

Kangye ya ce an kwato lita 325,990 na danyen mai, da lita 24,645 na gas, da lita 19,500 na PMS, da kuma lita 1,600 na man injina, sai kuma rushe matatun da suka hada da murhuna 86, da ramuka 181 da tankoki 18 da sauransu.

Ya ce a kokarin tabbatar da tsaro a sassan kasar nan, dakarun sojin sun kuma hallaka ‘yan ta’adda da dama, sun ceto wadanda akai garkuwa da su da kama wasu da ake zargi, tare da kwato bindigogi iri-iri, da bama-bamai da harsasai masu tarin yawa.

Leave a Reply