Daga Ƙarshe: Buhari ya Sauke Shugaban Shirin Inshorar Lafiya ta Ƙasa

0 434

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da muƙamin Babban Sakataren Shirin Inshorar Lafiya ta Ƙasa, NHIS, Usman Yusuf.

Matakin na Shugaban Ƙasa ya biyo bayan shawarwarin wani rahoton Kwamitin Tabbatar da Gaskiyar Lamari a kan NHIS ɗin.

Tuni Shugaban Ƙasar ya amince da naɗin Farfesa Mohammed Nasir Sambo a matsayin sabon Babban Sakataren Shirin da zai maye gurbin Mista Yusuf.

Shugaban ya kuma amince da rushe Hukumar Gudanarwa ta NHIS ɗin, ya kuma umarci Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa ya ci gaba da jan ragamar Hukumar Gudanarwar har a naɗa sabuwar Hukumar Gudanarwa.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya amince da naɗin Chikwe Andreas Ihekweazu a matsayin Darakta Janar na Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Ƙasa, NCDC.Naɗin ya yi dai-dai da tanade-tanaden Sashi na 11 (1) (3) na Dokar da ta Kafa Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Ƙasa ta 2018.

Leave a Reply

%d bloggers like this: