Da Yiwuwar Dakatar Da Tuƙa Adaidaita Sahu A Kano – Baffa Ɗan Agundi

0 393

Sabon shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano Dakta Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar hukumar KAROTA ta haramta tuka babur din Adaidaita Sahu a faɗin jihar Kano.

Baffa ya bayanna hakan ne a ofishinsa a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.

“Ko shakka babu, alamu na nuna yiwuwar dakatar da ci-gaba da aiwatar da sana’ar Adaidaita a fadin Jihar Kano baki daya, amma dai yanzu tukunna ba za mu ce komai ba akan wannan sana’a da Matasan wannan Jiha su ka yi wa rubdugu.”

Ya ƙara da cewa tuni dai jami’an tsaro masu aiki a jihar Kano su ke bincike domin tattaro bayanai akai kuma da zarar sun kammala binciken itama hukumar zata yanke hukunci.

A ƙarshe ya ce hukumar KAROTA a shirye take da ɗaukar kowanne mataki akan abin da take da hurumi domin kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: