Da yiwuwar Amurka ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare

0 214

Yayin da Donald Trump ke ci gaba da naɗe-naɗen muƙamai, kafofin watsa labaran Amurka sun yi hasashen cewa zai ba wa sanatan Florida, Marco Rubio muƙamin sakataren harkokin waje.

Mista Rubio ba ya goyan bayan tallafin soji da Amurka ke ba Ukraine, ya kuma goyi bayan tsare-tsaren Trump na Amurka ce farko, wanda hakan ke nufin ƙasar za ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare.

Yaƙin Ukraine shi ne yafi jan hankali a sabuwar gwamnatin, Trump ya bayyana cewa zai kawo ƙarshen yaƙin cikin ruwan sanyi sai dai bai bayyana hanyar da zai bi ba wajen tabbar da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: