Da Matsala: Mutane Kusan Miliyan 39 Ke Yin Bahaya A Waje

0 248

Wata Kungiya mai suna Water Aid tace kimanin mutane Miliyan 116 cikin akalla mutanen Najeriya Miliyan 200, basu da halin amfani da cikakken bandaki. Hakan yasa mutane Miliyan 38 da Dubu 800 daga cikinsu na yin bahaya a sarari.

Daraktar Kungiyar Water Aid a Najeriya, Evelyn Mere, ita ta fadi haka yayin kaddamar da wani shiri a Abuja.

Tace matsalar da ake fuskanta a bangaren ruwa, tsaftar muhalli da kiwon lafiya ya shafi makarantu, inda ta bayar da misali cewa kashi 50 cikin 100 na gabadaya makarantun Najeriya basu da ruwa da magewayi, yayinda kashi 50 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya basu da tsaftataccen ruwan sha, kuma kashi 88 cikin 100 na cibiyoyin, ba a tsaftace su kamar yadda ya kamata.

A cewar Evelyn Mere, akalla yara dubu 60 ne ke mutuwa kafin su fara zuwa makaranta a dalilin cututtukan da wadannan matsaloli ke haifarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: