Majalisar Wakilai ta amince da kudirin dokar gyaran haraji a yau Talata.
An aike da ƙudirorin hudu na gyaran dokar haraji zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa a watan Oktoba 2024.
A zaman majalisar na ranar Alhamis, Majalisar ta yi nazari tare da amincewa da rahoton Kwamitin Kudi na Majalisa, wanda ya yi aiki a kan kudirorin tare da la’akari da shawarwarin da ‘yan Najeriya suka gabatar.
Wadannan kudirori sun haifar da cece-kuce, inda shugabannin Arewacin Najeriya, Kungiyar Gwamnonin Najeriya da wasu kungiyoyin da ke da muradi suka nuna adawa da wasu sassan kudirorin.
- Comments
- Facebook Comments