Cutar Zazzabin Lassa Yayi Ajalin Mutane 154 A Fadin Jihohi 26

0 151

Hukumar kula da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) tace cutar zazzabin Lassa yayi ajalin mutane 154 a fadin jihohi 26 tun farkon shekararnan.

A wani rahoton halin da ake ciki kan cutar wanda aka fitar a jiya, hukumar tace jumillar mutane 897 ne aka tabbatar sun kamu da cutar yayin da aka samu mutane dubu 4 da 908 da aka yi zargin sun harbu da cutar cikin watannin.

Jihohin sun hada da Ondo, Edo, Bauchi, Taraba, Benue, Plateau, Ebonyi, Nassarawa, Kogi, Taraba, Gombe, Enugu, Kano, Jigawa, Oyo da Babban Birnin Tarayya da sauransu.

Rahoton yace kashi 72 cikin 100 na dukkan wadanda aka tabbatar sun kamu da zazzabin na Lassa sun fito daga cikin wadannan jihoshin uku na Ondo, Edo da Bauchi, yayin da aka samu kashi 28 cikin 100 daga jihohi 23 da aka tabbatar da samun wadanda suka harbu da cutar. Rahoton yace adadin wadanda ake zargin sun harbu ya karu idan aka kwantanta da adadin da aka samu cikin watannin a bara.

Leave a Reply