Cutar sankarau na neman zama ruwan dare a jihar Bauchi

0 25

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana cewa cutar sankarau na neman zama ruwan dare a jihar, bayan da aka samu fiye da mutum 218 da suka kamu da ita daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiyar Asali ta Jihar Bauchi, Rilwanu Mohammed, ya bayyana hakan a yayin wani taron wayar da kai kan mahimmancin sabon allurar rigakafin Measles-Rubella.

A cewarsa, an shirya taron ne domin ilimantar da matan shugabannin kananan hukumomi game da yadda za a gudanar da kamfen ɗin rigakafin da aka shirya yi a watan Oktoba.

Uwargidan gwamnan Bauchi, Aisha Mohammed, ta tabbatar da cewa mata za su taka muhimmiyar rawa a wannan yunkuri, domin hana cutar yaduwa tsakanin ƙananan yara da masu juna biyu.

Leave a Reply