Cikakken Bayanin Yadda Gwamnati Da Ƙungiyar Suka Cimma Matsaya

0 538

Bayan kwanaki suna zazzafar tattaunawa, Gwamnatin Najeriya da Ƙungiyar Ƙwadago sun cimma matsaya bisa tsarin da ya kamata a bi wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

An shafe tsawon watanni ana nuna rashin fahimta bisa yadda za a aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu tun a Afrilu, inda har Ƙungiyar Ƙwadago ta yi barazanar tafiya yajin aiki.

Ministan Ƙwadago Da Samar Da Aikin Yi, Chris Ngige, ya bayyana wannan labarin yarjejeniya da aka cimma wadda aka daɗe ana dako ranar Juma’a da sassafe jim kaɗan bayan tawagar da ya yi wa jagoranci ta kammala tattaunawa da Ƙungiyar Ƙwadago.

Taron tattaunawar, wanda aka fara da misalin ƙarfe 8:24 na dare ranar Alhamis, ya zo ƙarshe ne da misalin ƙarfe 3:00 na daren Juma’a.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne bisa yadda za a yi gyara a albashin ma’aikata, wanda dole a aiwatar da shi a dukkan hukumomi kamar yadda dokar sabon mafi ƙarancin albashin ta tanada.

Ƙungiyar Ƙwadago tana buƙatar ƙarin kaso 29 cikin ɗari ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 07 zuwa na 14, da kuma ƙarin kaso 24 cikin ɗari ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 15 zuwa na 17.

Amma, Gwamnatin Tarayya ta yi tayin ƙarin kaso 11 cikin ɗari ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 07 zuwa na 14, da kuma ƙarin kaso 6.5 cikin ɗari ga ma’aikatan dake kan matakin albashi na 15 zuwa na 17.

Sabuwar YarjejeniyaDa yake jawabi bayan taron tattaunawar tasu da ya ɗauki lokaci, Mista Ngige ya ce tsarin gyaran albashin da aka cimma yarjejeniya shi ne kamar haka:

“Ga waɗanda ke kan matakin albashi na farko, COMESS, mataki na 7, za su samu ƙarin kaso 23 cikin ɗari, matakin albashi na 8 za su samu ƙarin kaso 20 cikin ɗari, matakin albashi na 9 za su samu ƙarin kaso 19 cikin ɗari, matakin albashi na 10 zuwa na 14 za su samu ƙarin kaso 16 cikin ɗari, yayinda masu matakin albashi na 15 zuwa na 17 za su samu ƙarin kaso 14 cikin ɗari.

Waɗanda suke a tsarin albashi kashi na biyu, CONHES, CONRRISE, CONTISS da sauransu, mataki na 7 za su samu ƙarin kaso 22.2 cikin ɗari, mataki na 8 zuwa na 14 za su samu ƙarin kaso 16 cikin ɗari, mataki na 15 zuwa na 17 za su samu ƙarin kaso 10.5 cikin ɗari.

Ya ce kaso na uku na tsarin albashin ƙasar nan waɗanda su ne sojoji da jami’an tsaron da ba sojoji ba, su ma duk an sa su a cikin yarjejeniyar.“Tunda su ba sa cikin ma’aikatan gwamnati, za a faɗa musu nasu ta hanyoyin da suka dace.

Su ƙarinsu sirri ne”, in ji shi.Mafi Ƙarancin AlbashiShugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar sabon mafi ƙarancin albashi hannu tun a Afrilu. Amma aiwatar da ita ya samu tsaiko sakamakon rashin fahimta tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago da gwamnati kan yadda za a aiwatar da tsarin ƙarin albashin.

A taƙaice, matsalar ta fi shafar yadda ƙarin albashin zai kasance da kuma yadda za a gyara albashin ga ma’aikata daban-daban.

Hakan yasa ranar 14 ga Mayu, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai duba yadda za a biya sabon mafi ƙarancin albashin da kuma yadda gyaran albashin zai kasance, wanda shi ma ya kafa wani kwamitin ƙwararru da zai fito da tsarin yadda za a gyara albashin ma’aikatan gwamnati kamar yadda dokar sabon mafi ƙarancin albashin ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: