Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC tace zata shigo da tsarin dangwala kuri’a ta na’ura mai kwakwalwa a zabukan da ba na gama gari ba, farawa daga shekara mai zuwa.
Wannan na kunshe ne cikin kunshin dokokin hukumar mai shafuka 17 akan gudanar da zabuka lokacin annobar corona, dauke da sa hannun shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, da aka rabawa manema labarai a Abuja.
- Akalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara
- ‘Yan Kasuwa na nuna damuwar su kan faduwar farashin kayan Abinci
- Gwamnatin Jigawa ta bukaci jama’a da su kai rahoto kan duk dillalin da ke kokarin bata shirin Noma
- Hukumar JAMB ta cire wasu cibiyoyi guda 5 daga jerin wuraren gudanar da jarabawar UTME ta 2025
- Hukumar EFCC na neman jami’an CBEX ruwa a-jallo
Sai dai, hukumar tace ba za a dangwala kuri’a ta na’ura mai kwakwalwa ba a zabukan gwamnonin dake gabatowa a jihoshin Edo da Ondo.
Hukumar tace za tayi amfani da shafukan na’ura mai kwakwalwa wajen mika takardun neman shiga zabe daga jam’iyyun siyasa domin zabukan gwamnonin biyu.

Hukumar ta INEC tace lokacin zabukan Edo da Ondo, wadanda aka shirya yi a ranakun 19 ga watan Satumbar bana da 10 ga watan Oktoban bana,sanya takunkumin rufe fuska zai zaman tilas ga masu jefa kuri’a, da jami’an zabe da duk wanda ya halarci guraren zabe.