Cibiyar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Kasa, NCDC, ta ce kimanin mutane 753 ne suka sake kamuwa da annobar korona
Cibiyar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Kasa, NCDC, ta ce kimanin mutane 753 ne suka sake kamuwa da annobar korona a faɗin ƙasar a ranar Alhamis.
Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Legas suke, inda aka samu karin mutane 364 dauke da cutar.
Akwai kuma Akwa Ibom mai mutane 181, sai Oyo mutane 74 da kuma Rivers mutane 46.
Jihar Abia ma an samu mutum 38, Ogun mutum 24 da kuma Kwara mai mutum 20 sai Abuja nada mutum 12.
Sauran jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar sun haɗa da Ekiti mutum 10 da Delta 9 da Edo 7 Fitalo mutum 5, Imo 3 da kuma Bayelsa 1.
A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 180,661, sai dai mutane Dubu166,560 sun warke. Akwai kuma mutane 2,200 da suka mutu.
Kawo yanzu akwai kimanin mutane dubu 12,000 da suke cigaba da samun kulawa a cibiyoyin da hukumar ta ware domin kulawa dasu a Najeriya.
A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau’in cutar korona da ake kira Delta a Najeriya, wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.