CBN ya kara adadin kuɗin da bankunan kasuwanci za su mallaka a matsayin jari

0 299

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kara adadin kuɗin da bankunan kasuwanci za su mallaka a matsayin jari zuwa Naira biliyan 500.

CBN, ya ce dole ne kowane banki da ke hada-hada har a ƙasashen ƙetare ya kasance yana da jarin da bai gaza Naira biliyan 500 ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata takardar da daraktan sashen tsare-tsare da sanya ido kan ka’idojin kudi, Haruna Mustafa, ya sanya wa hannu.

CBN, ya bai wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi wa’adin watanni 24 domin cika wannan ka’ida. Wannan wa’adi zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2024, zuwa 31 ga Maris, 2026.

Leave a Reply

%d bloggers like this: