E-NairaBabban bankin kasa CBN, ya bukaci yan kasa da su rungumi tsarin amfani da Enaira, USSD da kuma tura kudi ta hanyar yanar gizo domin tafiya da tsarin takaita kudi a hannun jama’a.Babban bankin yace wannan hikimar da sannu zata zama dole a Najeriya duba da yadda kasar nan ke bi sahun kasashen duniya wajen amfani dai irin wadannan tsare-tsare.Mukaddashin daraktan sashen sadarwa na bankin Dr Abdulmumin Isa ne ya bayyana haka yayin taron ranar kasuwa ta musamman da aka shirya a Enugu karo 34.Ya kuma kara da cewa kasar nan baza ta bari a barta a baya ba wajen amfani da tsarin Kasuwanci na duniya dole ne a rungumi amfani da tsarin tura kudi ta yanar gizo.Dr Abdulmumin yace bankin CBN zaici gaba da samar da hanyoyi ga Najeriya da za suna amfani dasu wajen hada-hadar kudi a zamanance.Da yake jawabi dangane da sauya fasalin kudin na Naira yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da tsarin kafin a gudanar da shi, domin inganta tattalin arziki tare da tafiya kafada-da-kafada da sauran kasashen duniya.