Canjin da aka samu a zaben shugaba da mataimakin sa mabanbantan addinai ya sauya al’amura

0 295

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa canjin da aka samu a tsohuwar al’adar zaben shugaba da mataimakin sa mabanbantan addinai ya sauya al’amura a jihar.
Idan zamu iya tunawa dai SAWABA ta ruwaito cewa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar Kaduna, El-Rufai ya yi watsi da al’adar da aka dade ana yi na zaben Kirista a matsayin mataimakin gwamna daga kudancin jihar.
Hakan ne yasa wanda ya gaje shi Uba Sani ya dauki musulami a matsayin mataimakin sa.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da wani shiri na tarihin rayuwa da ritaya na Farfesa Ishaq Akintola, a Legas, El-Rufai ya yi nadama kan yadda zaben shugabancin da aka yi a jihar Kaduna ya jefa jihar cikin rikici.
Ya kara da cewa kamata ya yi a karfafa al’adun ‘yan kasa da suka shafi gudanar da mulki da kawo cigaba bawai Kallon addini a matsayin hanyar zaben shugaba da mataimakin sa ba.
El-rufai wanda shi ne babban mai jawabi kuma mai bayar da lambar yabo a wurin taron, ya ce zabin Tinubu-Shettima da akayi a matsayin shugaba da mataimakin sa daidai suke da zabin Abiola da Kingibe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: