Buhari Ya Tura Sojoji 6,000 Zuwa Zamfara

0 135

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin tura karin dakarun soji dubu shida zuwa Jihar Zamfara domin a rubanya ayyukan hukumomin tsaro na yaki da ta’addanci a Jihar.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya yi wa manema labarai da Yammacin ranar Talata.

Gwamna Matawalle ya ce wannan umarni na zuwa bayan wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu da ya shafe a birnin Abuja inda ya gana da shugaban kasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a kasar.

“Bayan tattaunawa da Shugaba Buhari da kuma manyan hafsoshin tsaro a Abuja, an cimma matsayar tura karin sojoji dubu shida zuwa Jihar Zamfara domin agaza wa kokarin da sauran jami’an tsaro ke yi na magance matsalolin tsaro a jihar.

“Nan ba da dadewa ba dakarun sojin za su iso jihar domin sauke nauyin da rataya a wuyansu sannan kuma muna matukar godiya ga Gwamnatin Tarayya a kan wannan mataki da ta dauka.”

“Saboda haka mu a matakin gwamnatin jiha, mun yanke shawarar daukar wadansu matakai da za su fara aiki nan take da suka hada da tabbatar da sarakunan gargajiya sun kasance a masarautunsu domin sanya idanun lura a kan duk wani shige da fice da yake wakana.”

“Sannan kuma mun hana goyon sama da mutum biyu a kan babur daya tare da haramta tafiyar babura a cikin tawaga ko ayari a dukkanin wani kwararo da sako na jihar,” in ji gwamna Matawalle.

A sanarwar da Gwamna Matawalle ya fitar, ya kara tabbatar da haramcin ayyuka ’Yan sa kai a jihar, inda yake cewa duk wanda aka samu da bindiga da sunan ya fito aikin ’yan banga za a hukunta shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: