Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya sunan sarki Abdullah Al-hussaini na Jordan a sabuwar cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa.
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar yau,inda ya kaea da cewa shugabannin biyu sun tattauna ta wayar tarho.
Garba shehu ya ce shugagannin biyu sun bayyana gamsuwar su wajen hadin Gwiwa kan matsalolin tsaro da suka shafi kasashen biyu, dama sauran batutuwan duniya.
Sanarwar ta kara da cewa sarkin na Jordan ya kira shugaba Buhari a waya domin taya shi murnar zuwan watan ramadan tare da yi masa Godiya biyo bayan sanya sunan sa da shugaba Buhari yayi a sabuwar cibiyar yaki da ta’addanci.
Sanarwar ta kara da cewa sarkin na Jordan Abdullahi ya bayyana aniyar sa ta zuwa Najeriya domin ya ziyarci shugaba Buhari kafin ya sauka daga Mulki.