Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi masu fafutukar raba kasar da su kauce wa yin haka ko kuma su gamu da fushin hukuma, yayin da yake cewa kasar za ta dore ne idan ta ci gaba da zama yadda take a yanzu.
Yayin da yake bude taron bikin cika shekaru 69 na haihuwar jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, shugaba Buhari ya ce a matsayinsa na tsohon soja wanda ya yi yaki domin ci gaba da dorewar kasar a matsayin kasa guda, ba zai bada damar rabewarta a karkashin mulkinsa ba.
Buhari ya ce duk da rikice-rikicen da ake samu da ke da nasaba da kabilanci jifa-jifa, ‘yan Najeriya sun yanke hukuncin ci gaba da zama tare ba tare da la’akari da banbancin kabila ko harshe da addini ba.
Shugaban kasar ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai fafutukar hadin kan kasa kamar yadda ya nuna a fafutukar siyasar da ya yi fice a kai lokacin da ya zauna a Majalisar Dattawa kafin soji su soke Jamhuriya ta 3 da kuma rawar da ya taka wajen ganin an bai wa Chief MKO Abiola mulki da jagorancin da ya yi a matsayin gwamnan Lagos na shekaru 8 tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.
Buhari ya ce a matsayinsa na sojan da ya yi yaki ya kuma san illar yaki da matsalolin da ke biyo baya wajen asarar sojoji da fararen hula, yayin da ake barin yara da mata da dattijai a baya.
Shugaban ya ce ya dace ‘yan Najeriya su yi nazari kan irin arzikin da Allah Ya yi wa kasar domin fadada batutuwan da za su hada kai da kuma tabbatar zaman lafiya.
Buhari ya yi jawabin ne a Abuja ta hoton bidiyo, yayin da ake gudanar da bikin a fadar gwamnatin Jihar Kano wanda ya samu halarta manyan ‘yan siyasa daga sassan kasar.