Buhari ya bayar da umarnin binciken harbin da aka yi ga masu zanga zangar #EndSARS

0 269

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bada umarnin bincike kan harbe harben da akayimasu zanga zangar #EndSARS lekki tollgate dake jihar Legas

Minstan wasanni da ci gaban matasa Sunday Dare ne, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da gidan telebijin na Arise a jiya Jumu,a.

Yayin harbin na wancan lokacin dai, mutane da dama sun samu raunuka yayin da wasu suka rasa rayukansu. A lokacin da aka bi yan zanga zangar da harbe harbe.

Da akayi masa tambaya dangane da yin shuru da shugaba Buhari yayi akan harbin na Lekki, a lokacin da yake yiwa yan kasar nan jawabi a ranar alhamis.

Ministan yace Buhari zaiyi magana idan aka gama bincike kan harbin da akayi musu nan gaba.

Kazalika ya kara da cewa gwamantin tarayyya ta amince da bukatun masu zanga zangar a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: