Buhari ya amince da cire Biliyan N10b domin Ƙidayar Jama’a

0 386

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin zunzurutun kudi har Naira Biliyan Goma N10b domin yin aikin ƙidayar jama’ar kasar nan.

Kuɗaɗen dai za a sakarwa hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) domin cigaba da ɗaukar alkaluman yankuna da kananan hukumomi 546 na ƙasar nan.

Muƙaddashin Shugaban hukumar Dr. Eyitayo Oyetunji ne ya shaidawa manema labarai hakan a shalkwatar hukumar.

A cewarsa, shugaba Buhari ya kuma amince da sakin wasu karin Naira NE.5b domin sakawa cikin kasafin 2021 don kammala wasu aiyukan da ake yi a yunkurin shirye-shiryen ƙidayar da za a gudanar nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: