Buhari Ya Aike Da Tawaga Domin Zuwa Ta’aziyya Ga iyalan Dansandan Da Ya Rasu A Zanga-zangar Yan Shi’a

0 269

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya aike da tawagar mutane 3 zuwa ta’aziyya ga iyalan mataimakin kwamishinan yansanda, Usman Umar, wanda ya rasu yayin hargitsi tsakanin jami’an ‘yansanda da yan mazhabar shi’a a Abuja.

Usman Umar, wanda kafin rasuwarsa, mataimakin kwamishinan yansandane a rundunar yansanda ta Babban Birnin Tarayya.

Tawagar mutane ukun ta kunshi babban jakadan shugaban kasa, Lawal Kazaure, sai babban mai taimakawa shugaban kasa kan kafafen labarai, Mallam Garba Shehu, sai kuma mai taimakawa shugaban kan harkokin cikin gida, Alhaji Sarki Abba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya kawo rahoton cewa, tawagar ta samu taryar dan’uwan mamacin, Usman Balele, wanda shima kwamishinan yansanda ne, da kuma matar marigayin, mai suna Busrah.

Kamfanin na Dillancin Labarai ya rawaito cewa, bayan Usman Umar, akwai wata ‘yar bautar kasa dake aiki da gidan talabijin na Channels, wacce ita ma ta rasa ranta a rikicin.

Wani harshin bindiga ne da aka harba, ya sameta, daga baya kuma ta mutu a asibiti.

Shugaba Buhari ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan 2, bayan faruwar lamarin ranar 23 ga watan Yuli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: