Buhari Ya Ƙalubalanci Ministocin Da Aka Rantsar Su Ɗora Kan Nasarorin Da Gwamnatinsa Ta Samu A Baya

1 484

Shugaba Buhari ya hori ministocin da su tashi tsaye wajen inganta tattalin arziki, yakar rashawa, tare da kafa Najeriyar da zata samar da ayyukan yi ga marasa aikinyi miliyan 20.

Shugaba Buhari sai ya bayar da muhimmanci ga bukatar tsaro, saboda ‘yan Najeriya su samu zama lafiya.Shugaban Kasar wanda ya amince cewa akwai matsaloli, amma sai yace ya kamata ‘yan Najeriya su lura da nasarorin da aka samu kawo yanzu.

Wasu daga cikin ministocin da ma’aikatun da aka tura su, sun hada da;

Mallam Adamu Adamu, daga jihar Bauchi, a matsayin Ministan Ilimi, da Isa Ali Pantami, daga jihar Gombe, a matsayin Ministan Sadarwa, da Suleiman Adamu, daga jihar Jigawa, a matsayin Ministan Albarkatun Ruwa, da Zainab Ahmed, daga jihar Kaduna, a matsayin Ministar Kudi.

Sauran sune, Sabo Nanono, daga jihar Kano, a matsayin Ministan Aikin Gona, da Janar Bashir Salihi Magashi, shima daga jihar Kano, a matsayin Ministan Tsaro, da Hadi Sirika, daga jihar Katsina, a matsayin Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Abubakar Malami, daga jihar Kebbi, a matsayin Ministan Shari’ah, da Babantunde Fashola, daga jihar Lagos, a matsayin Ministan Ayyuka da Gidaje, da Sale Mamman, daga jihar Taraba, a matsayin Ministan Wutar Lantarki, sai Abubakar D. Aliyu, daga jihar Yobe. Da sauransu.

  1. Alhaji Musa Muhammad says

    Masha Allah , Allah yayi jagora Sawaba Fm

Leave a Reply

%d bloggers like this: