Mai magana da yawun Tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari Malam Garba Shenu yace Buhari bai hana sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu ya binciki jami’an gwamnatinsa da ministocin sa ba.
Cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban Kasar ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami’an gwamnatinsa, labarai ne na ƙanzon-kurege.
Gabanin babbar salla ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke birnin Landan lokacin wata ziyarar ta ƙashin ƙai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin kuɗi na duniya da ya halarta a birnin Paris.
To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar, Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a ɗakin da suka gana, dan haka babu wanda ya san me suka tattauna.
Sanarwar ta kuma ce Buhari ya zaɓi fita daga Najeriya ne saboda gudun tsoma wa sabuwar gwamnati baki a al’amuranta. A farkon watan nan ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele daga kan kujerarsa, inda jami’an tsaron DSS suka kama shi tare da tsare shi.