Boss Mustapha ya umarci jami’an tsaro da suka kara kaimi wajen dakile yan bindiga a Adamawa.

0 174

A wani cigaban kuma sakataran gwamnatin tarayya Boss Mustapha yayi Allah-Wadai da mumman harin da aka kai kauyen Dabna dake karamar hukumar Hong na jihar Adamawa.
Harin wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa galibin su manoma da kuma dukiya mai yawan gaske.
Boss Mustapha cikin wata sanarwa da kakakin sa Willie Bassey, ya fitar, ya umarci jami’an tsaro da suka kara kaimi wajen magance ayyukan yan bindiga a jhar.
Ya kuma jajantawa gwamnatin jihar Adamawa da al’ummar kauyen Dabna bisa wannnan mummunan a hari da ka kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: