Bobrisky ya ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun da ta aike dashi gidan gyaran hali

0 243

Fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta, Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotu da ta same shi da aikata laifuka hudu da ke da nasaba da wulaƙanta takardun naira.

A ƙarar da ya shigar ta hannun lauyansa, Bimbo Kusanu, Bobrisky na neman kotu ta jingine hukuncin wata shida a gidan yari da aka yanke masa tare da neman kotu ta ba shi zaɓin biyan tarar naira dubu 50 kan duka laifukan da aka same da saikatawa.

A ranar 12 ga watan Afrilu nemai shari’a Abimbola Awogboro ya tabbatar wa kotun tarayya a Legas ta yanke wa Bobrsiky hukuncin watanni shida a gidan yari ba tare da zaɓi biyan tara ba saboda wulaƙanta naira.

A ranar 5 ga watan Afrilu, Bobrisky ya amsa aikata laifuka huɗu da hukumar EFCC ke tuhumarsa da aikatawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: