Bello Matawalle ya nemi sabbin hafsoshin soji da su kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

0 243

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi kira ga sabbin hafsoshin sojin Najeriya da suka samu karin girma da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.

Matawalle ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna ga sabbin jami’an, mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Mista Henshaw Ogubike, da aka rabawa manema labarai  ciki har da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya jiya a Abuja.

Ya ce karin girma da aka yi musu alama ce ta sadaukar da kai da kuma hidimtawa  kasa da suka yi.

Matawalle ya bayyana kwarin gwiwa kan iyawar su na yin shugabanci cikin gaskiya, jajircewa da kuma nagarta. Ya kuma kara jaddada aniyar shugaban kasa Bola Tinubu na samar wa rundunar soji kayan aiki da kuma dukkanin tallafin da suke bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: