Bayan Lafarwar Korona Gwamnati Na Cigaba Da Bude Filayen Jirgi

0 224

Gwamnati tarayya ta sanar da cewa a yanzu haka, an bude tashoshin jiragen sama 14 da ke fadin kasar nan, domin sufurin cikin gida na yan kasuwa.

Sanarwar hakan ta fito ta hannun Ministan Sufirin Jiragen Sama Hadi Sirika wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, tashshin jiragen sun dawo bakin aiki.

Sirika ya zayyano tashoshin jiragen saman, da suka hadar da na Murtala Muhammad dake Lagas, da filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja, da kuma na Malam Aminu Kano dake jihar Kano, sannan filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa na Portharcourt dake Omagwa.

Sauran sun hadar da filin jirgin Sam Mbakwe na Owerri, da kuma na  Maiduri, sai filin jirgin Victor Atta dake Uyo, da kuma na  Kaduna da Yola.

Sirika ya kara da cewa a kwai tashar Ekpo na Calaba da kuma Sultan Abubakar  dake Sokoto, sannan filayen jirgin sama na Birnin Kebbi da Yakubu Gowon da ke Jos, sannan tashar jirgin Benin dake Jihar Edo.

Ministan ya ce bayan kammala dukkan shirye-shirye, an amince da  tashoshin jiragen guda 14 su dawo bakin aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: