Bayan Dogon Jira, Buhari ya Zaɓi Ministoci

0 402

Tun bayan sake zabar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu aka yi ta zuba ido don ganin ko su wa zai sake zaba a matsayin Ministocinsa.

Shugaba Buhari dai yayi jan kafa a mulkinsa na farko, inda nadin Ministocinsa ya dauke shi har tsawon watanni shida, wanda hakan ya sanya har wasu ke kiransa da suna ‘Baba Go Slow’.

Yanzu dai haka wani rahoton da Jaridar Independent ta rawaito ya bayyana cewa Tuni shugaban kasar ya zabo Mutanen da zasu dafa masa wajen kai kasar nan ga gaci, kuma har ma tuni ya aikewa majalisar kasar nan don tantancewa, wanda suka ce zasu bayyana su a shafin yanar gizo don kowa ya gani a yau 2 ga watan Yuli.

Da zarar sunayen sun fito zamu wallafo muku su don ganewa idonku…

Leave a Reply

%d bloggers like this: