Batun ƴan fashi da makami da satar mutane na daɗa ƙamari a jihar Kano
Rundunar yan sanda a jihar kano tace ta kama mutane 245 da ake zargi da aikata laifuka a sassan jihar cikin kwanaki 40 na baya-bayan nan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da rundunar ta gudanar a helikwatar hukumar dake Bompai a jihar kano.
Yace wannan din na a matsayin wani bangare na yaki da ayyukan laifi, tsageranci da kuma daba, karkashin samamen da jami’an ‘yan sanda karkashin rundunar Puff-Adder, ke kai wa a kwaryar jihar domin kakkabe masu aikata laifi.
Wadanda aka kama din ana zarginsu da aikata laifufuka da suka hada da Fashi da makami, satar mutane domin neman kudin fansa, da barayin shanu, sai barayin motoci, da ‘yan daba, da masu ta’ammali da muggan kwayoyi.
Haka kuma dangane da lamarin yan fashin daji, rundunar yan sandan tace tayi nasarar kubutar da wasu mutane 6 da akayi Garkuwa dasu.