Basusukan da ake bin Najeriya ya haura dala biliyan 108.3

0 351

Ofishin kula da basussuka na kasa ya bayyana cewa basusukan da ake bin Najeriya ya haura dala biliyan 108.3 (wato naira triliyan 49.8).

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, ofishin ya bayyana cewa alkaluman da suka hada da kudaden da ake bin gwamnatocin tarayya da jihohi, baya daga cikin naira triliyan 22.7 da babban bankin kasa CBN ke bin gwamnatin tarayya.

Idan aka kwatanta, Jimillar Bashin a shekarar da ta gabata, a watan Disambar da ya gabata, ya kai naira Tiriliyan 46.2 sai dai tsakanin wancan lokaci, an sami karuwar basussukan gwamnatin tarayya da Jihohi da kuma birnin tarayya Abuja. Abinda yasa masana ke gargadin gwamnatin shugaba Bola Tinubu a kan ciyo basussuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: