Hukumomin lafiya a kasar Afirka ta Kudu sunyi kira ga mazauna lardin Gauteng da su yi taka tsantsan game da ruwan da suke sha yayin da adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a lokacin sanyi ya kai kusan 50.
Ƙungiyoyi al’umma sun bukaci ƙarin sa hannun gwamnati don inganta ingancin ruwa.
Galibin mace-macen da aka yi cikin makonni shida da suka gabata sun faru ne a yankin Hammanskraal, inda mazauna yankin suka ce sun shafe makonni suna fafatawa domin samun ruwa mai tsafta, amma an samu bullar cutar a fadin kasar.
A yankuna da yawa, ruwan famfo ba shi da tsabta kuma ana tilastawa mutane dogaro da motocin dakon gwamnati.
Cutar kwalara dai wadda gurbataccen abinci da ruwa ke haifarwa, na haifar da gudawa da amai kuma tana kuma iya sanadiyyar mutuwar mutum cikin sa’o’i idan ba a dauki mataki mai kyau ba.
- Comments
- Facebook Comments