Messi ba zai buga wasan Barcelona na karshe ba a gasar La Liga da za ta buga da Eibar a ranar Saturday domin ba shi damar hutawa kafin fara gasar Copa America, kamar yadda kungiyarsa ta bayyana.
Dan wasan Argentina da yake tattauna kwantaraginsa da Barcelona, an kuma ba shi umarnin kar ya buga atisaye a ranar Juma’a saboda kungiyar ta fita daga cikin wadanda za su iya cin gasar.
“Dan wasan zai samu hutu kafin fara gasar Copa America da za a fara a watan gobe, bayan kammala wannan kakar da ya zama daya daga cikin manyan yan wasan da suka buga wasa da yawa a wannan wasa,” a sanarwar da Barcelona ta fitar.
Tuni dan wasan mai shekara 33 ya buga wasa 47 a wannan kakar ya kuma ci kwallo 38, sai dai zamansa a kungiyar har yanzu na cikin kila wa kala saboda alakarsa da Manchester City inda zai iya haduwa da tsohon kocinsa Pep Guardiola.