Bankin NIRSAL sun fara horar da ma’aikatan aikin gona dubu 2 a jihar jigawa

0 342

Bankin tallafawa kananan masana’antu NIRSAL tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Jigawa sun fara horar da ma’aikatan aikin gona dubu 2 domin bunkasa harkar noman zamani a jihar.

A wajen kaddamar da shirin a Dutse, Manajan Daraktan Hukumar NIRSAL, Alhaji Abbas Umar Masanawa, ya ce an samar da shirin ne da nufin inganta amfani da dabarun noman zamani domin bunkasa sana’o’i.

Ya ce baya ga masu aikin noman alkama, shugabannin kungiyoyin manoman alkama karkashin shirin noman alkama na kasa na bana, suma suna halartar horon, kuma ana sa ran dukkansu za su isar da ilimin dabarun zamani ga sauran manoma domin samun nasarar girbi a bana.

Manajan daraktan wanda ya samu wakilcin Suleiman Ibrahim ya ce jami’an fadada ayyukan gona 355 da shugabannin kungiyar manoma 706 daga kananan hakumomin Kiyawa da Birnin Kudu da Ringim da Hadejia da kuma Kazaure ne suka halarci kashin farko na horaswar. Kwamishinan aikin gona da raya karkara na jihar Jigawa Muttaka Namadi ya bayyana cewa gwamnatin jihar a shirye take ta hada karfi da karfe domin inganta ayyukan noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: