Bankin Duniya ya amince ya bai wa Jamhuriyar Nijar tallafin CFA biliyan 214

0 167

Bankin Duniya ya amince ya bai wa Jamhuriyar Nijar tallafin CFA biliyan 214 domin bunkasa fannin noma da kiwo a kasar.

Tallafin ya kai Dalar Amurka miliyan 350 na zuwa ne a daidai lokacin da farashin kayan abinci yake ci gaba da tashin gwauron zabi.

Saboda haka ya yi hasashen bayar da tallafin a bangaren noma da zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci a kasar.

Hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar da ke fama da matsalar karancin abinci da ta tsadar rayuwa.

A cewar bankin kashi 80 cikin 100 na al’ummar kasar sun dogara ne da fannin noma domin samun kudaden shiga. Ya kara da cewa kashi 40 na kudaden Jamhuriyar Nijar na zuwa ne daga bangaren noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: