Ban san ko zan tsaya takarar shugabancin kasa a shekarar 2027 ba – Atiku

0 77

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa bai san ko zai tsaya takarar shugabancin kasa a shekarar 2027 ba. 

Atiku ya yi wannan bayani ne a wata hira da zai yi a wani shirin talabijin mai suna *Untold Stories* tare da Adesuwa Giwa-Osagie.

A kwanakin baya, Atiku ya sanar da kafa wata hadakar jam’iyyun adawa domin kwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaban  2027.

Sai dai har yanzu ana ta cece-kuce kan wanda zai jagoranci wannan hadaka kuma ya zama dan takarar shugabancin kasa.

Daga cikin sunayen da ake hasashe sun hada da: 

Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP)  da Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna 

Atiku, wanda ya taba yin takarar shugaban kasa sau shida, bai bayyana karara cewa ba zai sake takara ba, wanda ke nuna akwai yiwuwar sake tsayawarsa.  Haka nan, ya nuna rashin jin dadinsa da yadda shugabanni ke tafiyar da kasar.

Leave a Reply