Bayan ikirarin da Gwamnatin tarayya tayi cewa farashin man fetur a kasar nan na daga cikin mafiya sauki a nahiyar Africa, kungiyar kwadago ta kasa hadi da wasu kungiyoyin fararen hula, sun bayyana hujjar da gwamnatin ta rika a matsayin maras tushe.
A wata hira da yan jaridu, Shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba, yace kamata yayi gwamnatin ta alakanta karin farashin man da saukar darajar Naira, da kuma tsarin albashi mafi kankanta da ake biyan ma’aikata.
- Hisba ta kai samame wasu gidajen sayar da barasa uku a jihar Jigawa
- Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Jihar Nasarawa
- Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa
- Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta
- Za’a dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya
Suma dai wasu rassan kungiyar na jihohi sunce karin farashin man da na kudin wuta, ya sanya sabon tsarin albashi mafi karanci na naira dubu 30 a matsayin anyi ba ayi ba.
A ranar litinin din da ta gabata ne dai ministan yada labarai da raya al’adu Lai Muhammad yace duk da karin kudin man da akayi, farashin kayan masarufi a kasarnan kawo yanzu, na daga cikin mafiya rangwami a fadin Africa.