Badaru Abubakar yace zai hada kai da masana tsaro domin yaki da matsalar tsaro a kasar nan

0 565

Sabbin Ministocin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu ya rantsar a jiya sun fara bayyana ajendodin da suka sa a gaba.

Inda, Ministan yada labarai Muhammad Idris yace ma’aikatar sa bazata ta fadi karya ba domin kare muradan gwamnati.

Da yake jawabi jim kadan bayan shigar sa Ofis, yace ma’aikatar sa mai adalci da gaskiya yayin bada bayanan kasa.

Muhammad Idris ya kuma bukaci Yan Najeiya da su kauracewa labaran karya su tabbatar da ingancin su kafin sanar da jama’a.

Shima Ministan shari’a na gwamnatin Tarayya Lateef Fagbemi ya jaddada shirin na yin aiki yadda ya kamata a fannin shari’a,inda bukaci ana bin dokokin kasa. Shima Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar, yace zai hada kai da masana tsaro domin yaki da matsalar tsaro a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: