Babban Matakin Da Mutanen Jigawa Ya Kamata Su Dauka Don Gujewa Zazzabin Cizon Sauro

0 221

Shirin yaki da zazzabin cizon sauro na jihar Jigawa ya shawarci al’umma dasu tabbatar da tsaftace muhallansu domin kare kai daga kamuwa da zazzabin cizon sauro na malaria.

Jami’in kula da shirin na jiha Malam Bilya Haruna ya yi wannan kiran a bikin ranar yaki da malaria ta bana.

Yace tsaftar mahalli da share kwatoci da magudanan ruwa suna taimakawa wajen kashe kwayoyin yaduwar sauro.

Mallam Bilya Haruna ya kara da cewa akwai bukatar iyalai su kula da tsaftar muhallinsu domin barin datti a gida yana haddasa samun kwayoyin sauro mai yada malaria.

Ya shawarci al’umma musamman mazauna yankunan karkara dasu dauki akidar tsaftar muhalli domin gudun kamuwa da cututtuka.

Inda kuma ya yi kira ga al’umma dasu rinka zuwa asibiti domin yi musu gwajin cutar malaria.

Leave a Reply

%d bloggers like this: