Babban mai shari’a na kasa yayi kiran gaggawa ga alkalin jihar Jigawa domin bada bahasi akan rikicin jam’iyyar PDP
Babban mai shari’a na kasa, Justice Tanko Muhammad yayi kiran gaggawa ga alkalan Jihohin Rivers, Kebbi, Cross Rivers, Anambara, Jigawa da kuma jihar Imo, domin su bada bahasi akan alkalan da suke karkashin su.
A satin da ya gabata kotuna guda biyu sunyi sharia’a kan rikicin da ya kunno kai a jam’iyyar PDP.
Cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 30 ga watan agustan wannan shekarar, babban mai shari’ar ya kira alkalan domin bayani dangane da shari’o’in da ake na rigin-gimun jam’iyyun.
Justice Tanko Muhammded ya bayyana cewa yayiwa alkalan kiran gaggawan ne, domin yaji irin cigaban da aka samu dangane da irin shari’un da ake gudanarwa, a matsayin sa na babban mai shari’a na kasa.
Kazalika ya ja kunne dukkanin alkalai da gudanar da adalci a shari’ar.