Babban Bankin Kasa CBN ya amince da yarjejeniyar buga kudaden kasar Gambia.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya amince da bukatar daga Gwamnan babban bankin kasar Gambia, Buwa Sa’idi, wanda ya jagoranci wata tawaga wacce ta ziyarce shi a yau.
Emefiele yace Najeriya na da karfi sosai na buga kudade kasancewar kasar tana buga kudade tun daga shekarar 1960.
Tunda farko, Gwamnan babban bankin Gambia yace kasarsa na fuskantar karancin takardun kudade kuma tana so ta koyi yadda zata kula da takardun kudadenta ta hanyar koyi daga dumbin kwarewa da gogewar Najeriya.
Yace a halin yanzu, sun nemi a buga musu takardun kudade na shekara 2 a kasar waje amma suna duba yiwuwar buga kudaden daga Najeriya muddin kasarnan ta amince.
A nasa bangaren, kamfanin buga takardun kudade na Najeriya yace a shirye yake muddin dukkan bangarorin suka amince da yarjejeniya.