Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Benson Upah, ya ce katsalandan da gwamnoni ke yi a tattaunawar da ake yi kan mafi karancin albashin ma’aikata ya sabawa ka’ida kuma lamari ne da baza’a lamunta ba.
NLC, na bukatar gwamnoni suyi gum da bakin su saboda basu da ikon yin katsalanda ga tsarin shawarwarin mafi karancin albashi na kasa.
Haka kuma, Upah ya yi watsi da gargadin gwamnatin tarayya na yin murabus da yawa a cikin ma’aikatan gwamnati a matsayin “wani mataki ne na cin zarafi.”
- Comments
- Facebook Comments