Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, yace gwamnatin tarayya tana saka matasa a wajen tsare-tsaren kudirori.
Yemi Osinbajo ya fadi hakane ranar Juma’a a Abuja, yayin liyafar cin abincin dare a fadar shugaban kasa, da aka shiryawa taron samawa matasa aiki ta duniya, na kungiyar kwadago ta kasa da kasa, domin karrama Darakta-Janar na Kungiyar Kwadagon ta Kasa da Kasa, Mista Guy Ryder.
Mista Ryder yazo Najeriya ne domin halartar taron samawa matasa aiki ta duniya na kungiyar kwadago ta kasa da kasa, wanda kasashe sama da 60 suka hallara, domin tattauna kalubalen samar da aiki ga matasa.
Guy Ryder ya kuma ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban Kasa, ranar Alhamis.
Yemi Osinbajo yace, sauraron matasa masu karancin shekaru, na magana akan damarmaki, yana sanyaya masa zuciya.
Da yake mayar da jawabi, Guy Ryder, ya godewa yan Najeriya bisa karramawar da akayi masa. Yace ya tattauna da yan Najeriya daban-daban, ciki harda kungiyoyin kwadago, inda ya kara da cewa, akwai kyakykyawar alaka tsakanin kungiyar kwadago ta Najeriya da kungiyar kwadago ta kasa da kasa.