Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana shirinsa na maraba da Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a matsayin sabon shugaban kasa, yana mai tabbatar da cewa za a mika mulki ga sabuwar gwamnatin a ranar 29 ga watan Mayu.
Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne a wannan mako a lokacin da yake musayar gaisuwar Sallah a wata hirar wayar tarho da ya yi da shugaban kasar mai jiran gado, Sanata Bola Tinubu.
Shugaba Buhari da Bola Tinubu sun godewa Allah da ya nuna musu wannan rana tare da yin addu’ar Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarnan.
Shugaban mai ci wanda tun da farko ya gudanar da Sallar Idi Abuja, ya amsa tambayoyi daga manema labarai, inda ya tabbatar da cewa dimokuradiyya na da makoma mai kyau a Najeriya.
Shugaban kasar ya ce tabbacin da yake da shi ya ta’allaka ne kan yadda ‘yan Najeriya ke da ra’ayin kare dimokradiyya daga duk wata barazana.
- Comments
- Facebook Comments