Ba lallai ba ne haɗakar ƴan siyasar Najeriya ta yi tasiri – Shekarau

0 53

Ɗaya daga cikin jagororin siyasa a arewacin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Kano Malama Ibrahim Shekarau, ya ce ba lallai ba ne haɗakar da wasu manyan ƴan siyasar ƙasar ke yi don tunkarar zaɓen 2027 ta yi wani tasiri ba.

Shekarau ya bayyana haka ne a zantawarsa da BBC, inda ya ce saɓanin haɗakar da suka jagoranta a 2015 da ta kai ga kawar da mulkin PDP a shekara 16, a yanzu ƴan siyasa ne kawai ke ganawa a tsakaninsu, ba da yawun jam’iyyunsu ba.

A game da zargin ko dai yana yi wa APC aiki ne, Shekarau ya ce ba haka ba ne, “ai idan ina so zan yi aiki da APC, zan je kai-tsaye ne. A cikin shugaban ƙasa da gwamnoni babu wanda idan ina son ganinsa ba zan iya ba.”

“Ni dai shawara na bayar cewa yunƙurin nan zai yi nasara ne kawai idan an jawo jam’iyyun hamayya an tafi tare da su,” in ji shi.

– BBC Hausa

Leave a Reply